Gwajin makamai a Iran
July 2, 2012Kamfanin dillancin labarun Iran na IRNA ya rawaito cewa dakarun juyin juya halin ƙasar zasu ƙaddamar da wata atisaya, ko kuma gwajin makamai ranar litini, a abunda ta kwatanta da gargadi zuwa ga ƙasashen yamma. Kamfanin dillancin labarun ya ce wannan atisaya sai haɗa da harba makamai masu dogon zango zuwa sansanonin da aka gina da suffan sansanonin ƙasashen ƙetare.
Ana sa ran ƙaddamarwa da duk wannan ne, wuni guda bayan da takunkumin da Turai ta sanya mata na fitar da man fetur ya kama aiki.
Daga yanzu dai duk kwangilolin fitar da man fetur ɗin da ƙasar ta sanyawa hannu tare da ƙungiyar mai mambobi 27 sun mutu.
Ƙasashen sun sanyawa Iran wannan takunkumi ne domin matsa mata lamba kan shirin makamashin nukiliyar ta. Ƙasashen yamman na zargin gwamnati a Tehran da yunƙurin sarrafa makaman ƙare dangi, zargin da ta ƙaryata ta ce shirinta na nukiliya na dalilan zaman lafiya ne tsantsa.