Gwajin makaman Iran masu linzami ya yi nasara
January 2, 2012Ƙasar Iran ta bayyana cewa ta yi nasasa a gwajin da ta yi a ƙarshen mako na wasu makamai masu linzami da ta ƙera. Wannan kuwa ya zo ne kwanaki ƙalilan bayan da babban jami'inta da ke kula da harkokin nukilya wato Said Jalili, ya yi fatan ganin cewa an farfado da tattaunawa tsakanin Iran da ƙungiyar Gamayyar Turai game da shirin nukiliya na ƙasarsa.
Dama dai Iran ɗin ta yi gwajin wasu makamai masu cin dokon zango a yankin Gulf, a wani mataki na ci gaba da atisayen makamai da ta sa a gaba. Kana ta yi barazanar rufe mashigar ruwan Hormuz, matiƙar ƙasashen yammacin duniya suka aiwatar da shirinsu na sanyawa ƙasar ta Iran ƙarin takunkumin karya tattalin arziki, sakamakon kunne uwar shegu da ta ke yi ga kiraye kirayen da ake yi mata na watsi da shirinta na Nukiliya.
Sai dai a wani mataki na mayar da martani, shugaba Barack Obama na Amirka ya rattaɓa hannu akan wata doka da ta tanadi ƙaƙa takunkumi kan man da Iran da ke sayarwa da kuma kawo ƙarshen ma'amalla da ke tsakanin ƙasarsa da Iran a fannin harkokin bankuna.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi