Gwamnan Jihar Bayelsa Dapriye Alamieyeseigha ya yi shigar mata ya tsere bayan da aka ba shi beli
November 21, 2005Gwamnan Jihar Bayelsa a tarayyar Nigeria Dapriye Alamisiya wanda yan sandan suka kame a birnin London saboda samun sa da hada hadar kudade ba bisa kaída ba, ya ranta a na kare bayan da aka bada belin sa. A ranar 15 ga watan Satumban shekara ta 2005, yan sandan Britaniya suka kame Alamisiya a filin jirgin saman Heathrow a London dauke da tsabar kudi dala miliyan 3.2 wadanda ya kasa bayanin asalin su. An bada belin sa ne bayan karbe fasfo din sa, tare da sharadin ba zai tsere ba har ya zuwa lokacin da zaá gurfanar da shi gaban shariá. Sai dai abin mamaki, a ranar Litinin din nan, kwamishinan yada labarai na Bayelsan Oronto Doughlas ya sanar da cewa gwamnan ya komo gida kuma har ma koma bakin aiki. A waje guda kuma shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Nigeria Alhaji Nuhu Rubadu yace gwamnan yayi amfani da takardu ne na jabu tare da yin shigar mata wajen sulalewa daga kasar ta Britaniya. Alhaji Nuhu Ribadu ya baiyana cewa wannan babban abin takaici ne ga kasar. Yana mai cewa ba zasu yi kasa a gwiwa ba, zasu cigaba da dukkan kokari har sai an tabbatar da cewa an gudanar da adalci. Shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo ya bukaci yan majalisar dokokin Jihar Bayelsan su tsige Alamisiye domin gurfanar da shi gaban shariá, sai dai kuma yan majalisar sun ki nuna karsashi ta yin hakan.