Gwamnati Burma ta yi barazanar yanke hukunci mai tsanani ga shugabanin zanga-zanga
October 9, 2007Gwamnatin mulkin soja a ƙasar Burma ,ta yi barazanar yanke hukunci mai tsanani, ga ragowar mutane fiye da dubu ɗaya, wanda a halin yanzu ke tsare a kurkuku.
Gwamnatin ta capke wannan pirsinoni, a sakamakon zanga-zangar gama gari da ta ɓarke a ƙasar, wace kumata yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Saidai gwamnati ta bayyana matsayin ta, na ganawa da shugabar yan adawa ta ƙasar, Aung San Suu Kyi.
A game da haka, har ma ta naɗa wani jami´in soja, wanda zai kulla da mu´amila tsakanin Su Kyi, da gwamnatin.
A ɗaya hannun kuma jiya ne, komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya gudanar da sabuwar mahaura, a game da matakin da ya ke shirin ɗauka, a kann ƙasar ta Myanmar.
Ƙasar Sin, da sauran wasu ƙasashen membobin komitin sulhu, sun gudanar da kwaskawarima ga buƙatar France Ingla, da Britania ta ɗaukar hukunci mai tsanani ga magabatan Myanmar.