'Yan adawa na zanga-zanga a Senegal
March 23, 2023Talla
Shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya ce gwamnati za ta yi duk abin da ya dace na matakan tabbatar da doka da oda a kasar, yayin da ake ci gaba da samun zanga-zangar kan shair'ar da ake yi wa jagoran 'yan adawa na kasar Ousmane Sonko, lamarin da ya janyo mutuwar mutum daya.
An dai samu tashe-tashen hankula a birane da dama kan shair'ar da ake yi wa Sonko kan zargin bata suna, abin da ake ganin zai shafi takarar da jagoran 'yan adawa ke shirin yi a zaben shekara mai zuwa ta shekara ta 2024. Ana zargin dan dawan da kalaman bata suna ga ministan a gwamnatin kasar.
Ita dai Senegal tana cikin kasashe masu kwanciyar hankali na siyasa a yankin yammacin Afirka.