Gwamnati ta tabbatar da tsadar rayuwa a Ghana
October 12, 2022Talla
Hukumar ta ce a yanzu sabbin alkaluman tsadar rayuwar sun kai kashi 37% kamar yadda ya bayyana cikin watan jiya na Satumba, sabanin kashi 33.9% da aka gani a watan Agustan bara.
Babban bankin kasa a Ghana dai ya yi karin kudin ruwa da kaso 10% a bana, matakin da ya ce ya dauka ne da nufin rage tashin farashin kayayyaki da ma taimaka wa faduwar darajar kudin kasar wato cedi.
Sai dai kudin na cedi ya kasance kudi mafi tabarbarewa a Afirka tun a farkon wannan shekarar, kamar yadda bankin duniya ya nunar a makon jiya.
A halin ma da ake ciki kudaden ajiyar ko-ta-kwana da Ghanar ke da su, sun koma dala biliyan 2.7 cikin watan Satumba da ya gabata, maimakon dala biliyan 6.1 da take da su cikin watan Janairu.