1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati Burundi ta kauracewa taron zaman lafiya

Ramatu Garba Baba
October 25, 2018

An dage zaman taron sasanta rikicin kasar, bayan da wakilan gwamnatin suka sanar da kauracewa zaman da aka shirya a tsakanin bangaren gwamnati dana 'yan adawa a birnin Arusha na kasar Tanzaniya.

https://p.dw.com/p/379zV
Tanzania Arusha Friedensgespräche mit ehemaligem Präseidenten Bejamin Mkapa
Hoto: DW/C. Ngereza

Sanarwar gwamnati ta bayar da dalilin kauracewa taron ganin ya zo daidai da ranakun da Burundi ke nuna alhinin kisan gillar da aka yi wa wasu tsofin shugabanin kasar a can baya. An shirya taron da kasar Tanzaniya ta dauki nauyinsa da zummar cimma daidaito a tsakanin bangaren gwamnati da jam'iyyar adawa, bayan da rikici a tsakaninsu ya ki ci-ya ki cinyewa, ana ganin yin hakan zai sa a sami hadin kai don tsara yadda za a tafiyar da babban zaben kasar na shekarra 2022.

Kawo yanzu dai, gwamanatin Burundi ta aki amincewa da bangaren adawa inda ta ayyana jam'iyyar a matsayin kungiya ta 'yan ta'adda. Wannan shi ne karo na biyar da ake zaman taron sulhunta rikicin kasar ta Burundi. Idan ba a manta ba, kasar ta tsunduma cikin rikicin siyasa a lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya nemi yin tazarce a karo na uku, Rikicin da ya biyo bayan yunkurin ya lakume rayuka akalla dubu daya da dari biyu baya ga daruruwan da suka rasa matsuguninsu.