1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Gwamnati ta yi wa fursunoni afuwa

July 18, 2023

Shugaban gwamnatin soja na Chadi Mahamat Idriss Deby Itno,ya sa hannun a kan kudirin yin afuwa ga fursunoni 110 da aka tsare bayan wata zanga-zanga da aka gudanar a birane daban-daban na kasar a watan Oktoban bara.

https://p.dw.com/p/4U2aY
Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

An samu wadanda aka yi wa afuwar wadanda galibinsu matasa ne da aikata laifin gudanar da jerin gwano ba tare da izini ba, wanda ya jikkata jami'an tsaro da kuma kone wasu kadarorin gwamnati. Sama da mutane 600 ne aka kama bayan tarzomar da ta barke a ranar 20 ga watan Oktoban 2022 a Chadi, ciki har da yara masu kasa da shekaru 18  inda aka iza keyarsu i zuwa wani gidan kaso da ke cikin Sahara a tazarar mil 600 da N'Djamena babban birnin kasar.

Dama dai a watannin da suka gabata, gwamnatin mulkin soja ta Chadi ta yi afuwa ga wadansu daga cikin fursunonin da aka tsare. Sai dai har yanzu wasu iyalai na dakon 'ya'yansu da suka yi batan dabo.