1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Faransa za ta fara tattaunawa da masu bore

Mohammad Nasiru Awal LMJ
December 3, 2018

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya umarci Firaminista Edouard Philippe da ya fara tattaunawa da wakilan masu boren.

https://p.dw.com/p/39KvN
Frankreich Protest Vandalismus Arc de Triomphe
Hoto: Reuters/S. Mahe

Bayan mummunar arangama da aka yi tsakanin masu bore da ke adawa da karin harajin kudin man fetir da 'yan sanda a birnin Paris na kasar Faransa, yanzu gwamnatin kasar ta nuna shirin zama kan teburin tattaunawa da masu zanga-zangar.

Shugaban kasa Emmanuel Macron ya umarci Firaminisa Edouard Philippe da ya fara tattaunawa da wakilan masu boren don gano bakin zaren warware takaddamar. Akalla mutane 263 suka ji rauni yayin boren na ranar Asabar a fadin kasar, sannan a birnin Paris an shiga rudani.

Sai dai a cewar mataimakin ministan cikin gidan Faransa, Laurent Nunez gwamnati ba ta da niyyar kafa dokar ta-baci saboda boren. Ministan ya fadi haka ne a wannan Litinin bayan kiraye-kirayen da kungiyoyin 'yan sanda suka yi na a ba su karin iko don shawo kan zanga-zangar.

Su dai masu zanga-zangar na neman gwamnati ta rage kudin haraji sannan ta kara yawan albashi mafi karanci da kudin fansho.

A ranar Talata ake sa rai za a zauna kan teburin shawarwari tsakanin gwamnati da wakilan masu bore.