Gwamnatin Girka ta gabatar da kasafin kuɗin baɗi
October 3, 2011Gwamnatin ƙasar Girka ta gabatar da kasafin kuɗinta na baɗi a gaban majalisar dokoki, a dai-dai lokacin da kasar ta mamaye kanun labaran duniya. Ministocin kuɗin ƙasashen da ke amfani da kudin euro na ganawa a ƙasar Luxemburg a yau, domin tattaunawa yadda za su miƙawa ƙasar Girka ƙarin bashi. An dakatar da baiwa ƙasar Euro biliyan takwas tun a wata guda. Sepetoci daga hukumar bada lamuni ta duniya wato IMF da bankin Turai da kuma ƙungiyar Tarayyar Turai na can a birnin Athens domin gudanar da bincike, ko za a iya miƙawa Girka rigowar kudin da aka yi mata alƙawari. Gwamnatin ƙasar ta Girka a jiya ta amince ta kori ma'aikata dubu 30 a wani ɓangaren cike giɓin kasafin kudinta. Akasarin ma'akatan da aka kora sun yi kusan ritaya ne, gwamnati za ta koresu ta biyasu yan kudi ƙalilan. Kundin tsarin mulkin ƙasar Girka ya kare ma'aikata daga kora a wurin aiki. Su dai ma'aikatan ƙasar sun ƙuduri shiga yajin aiki a gobe Talata da yardan mai duka.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu