Gwamnatin Iran, na karaɓar baƙwancin wani taro, kan nemo hujjojin gaskanta ko kuma ƙaryata batun nan na halaka Yahudawa a yaƙin duniya na biyu.
December 11, 2006A yau ne aka buɗe wani taro da ake ta ƙorafi a kansa, a birnin Teheran na ƙasar Iran, don tattauna batun nan na Holocaust, ko kuma halaka ɗimbin yawan Yahudawa da aka yi a loakcin yaƙin duniya na biyu a Jamus. Gwamnatin Iran, wadda ke karɓar baƙwancin taron, ta ce burinsa ne dai ya bai wa masana tarihi na cikin gida da na ƙetare, damar yin nazari mai zurfi don gano wai shin gaskiya ne wannan ɗanyen aikin ya auku ko kuwa shiri ne dai na ƙasashen yamma da masu bin aƙidar Zionisanci, suka ƙikiro? Manazartan tarihi fiye da 60 daga ƙasashen Yamma, a cikinsu har da shahararren ɗan ƙasar Austreliya, haifaffen Jamus ɗin nan Frank Toeben, tare da takwarorinsu na Iran ne za su shafe kwanaki biyu suna tatttaunawa da musayar yawu kan wannan batun, a birnin Teheran. Shugaban ƙasar Iran, Mahmoud Ahmadinijad, ya sha nanata cewa, labarin da ake ta yayatawa, na kisan da aka yi wa Yahudawa kimanin miliyan 6 a ƙarƙashin mulkin Nazi a Jamus, a lokacin yaƙin duniya na biyu, ba kome ba ne illa almara. Amma duk da haka, Iran ɗin ta yi watsi da sukar da ake yi mata, na nuna ƙyama ga Yahudawa. Ta ce kimanin Yahudawa dubu 25 ne ke zaune a halin yanzu a ƙasar.
Ƙasashe da dama dai, musamman na Yamma, sun yi ta sukar taron na birnin Teheran da babban murya. A ƙasashe da dama na Turai dai, musamman a Jamus da Austriya, laifi ne a ƙaryata aukuwar Holocaust ɗin, wato kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa kimanin miliyan 6 a lokacin mulkin Nazi a yaƙin duniya na biyu.