Gwamnatin Jamus ta kara kudaden taimakon 'yan gudun hijira
September 7, 2015Talla
Dubban 'yan gudun hijira na ci gaba da tururuwa zuwa kasar Jamus ta Jihar Bavariya, wasu da jiragen kasa, wasu motoci, yayin da wasu ke takawa da kafa, bayan ficewa daga kasar Hangari.
Gwamnatin kasar ta Jamus ta ware kimanin Euro milyan dubu shida domin kula da 'yan gudun hijiran. An amince da shirin tsakanin manyan jami'an gwamnatin hadaka. Euro miliyan dubu uku yana cikin kasafin kudin shekara ta 2016, yayin da sauran miliyan dubu uku za a yi amfani da su wajen taimaka wa jihohi da kananan hukumomi.
Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya nemi iyalai a kasashen Turai mabiya darikar su dauki dawainiyar 'yan gudun hijira. Tuni fadar ta Vatikan ta ba da misali.