1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin mai ci a Pakistan na rawa

January 12, 2012

A kasar Pakistan ana zaman dar-dar biyo baraka tsakanin rundunar soji da masu mulkin farar hula, inda aka rabu gida biyu tsakanin masu marawa soji da na farar hula

https://p.dw.com/p/13hzG
Asif Ali Zardari, husband of slain Pakistan's opposition leader Benazir Bhutto thanks supporters for their condolences at his house in Naudero near Larkana, Pakistan on Tuesday, Jan. 1, 2008. Pakistan's election commission said Tuesday that unrest following the killing of Benazir Bhutto would almost certainly force the postponement of the scheduled Jan. 8 elections, despite opposition threats of street protests if the poll is delayed. (AP Photo/Shakil Adil)***Zu Matthay, Partei als Familienangelegenheit - Asif Zardari im Porträt***
Shugaban kasar Pakistan, Asif Ali ZardariHoto: AP

A kasar Pakistan gwamnati Asif Ali Zardari na cikin tsaka mai yuwa, kan batun wata wasika da ya rubutawa kasar Amirka da ta kare shi daga juyin mulkin sojoji, wanda kuma aka tseguntata. An dai yi ta rade-radin cewa Zardari zai sauka daga mulki tun dawowa daga jinya a Dubai. A jiya an sallami ministan tsaro kuma babban kusa a sojojin kasar masu iko mai karfi a Pakistan. A yau babban hafsan hafsoshin kasar ya kira taron kwamandojin sojin kasar don ganawar gaggawa, wata majiyar soji tace, suna son Zardari ya sauka daga mulki, amma ta hanyar doka ba juyin mulkin soji ba. Yanzu haka dai kotun kolin kasar na bincike kan wasikar da ya rubutawa Amirka, kuma tabbas in an samu shugaban da laifi to zai sauka daga mulki, haka ma kotun na binciken wasu manyan jami'ai a jam'iyar shugaba ciki har da firayim ministan Yusfu Raza Gilani, wadanda za a iya saukar da su, idan aka same su da laifi. A kasar Pakistan dai sojoji na da karfin fada aji, kuma basa barin duk wani dan siyasa ya shiga harkarsu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu