Gwamnatin Najeriya ta nada sabon Sefeto janar na yan sandan kasar.
January 25, 2012Alummar anguwar Sheka dake yankin karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun fara dawowa cikin hayyacinsu, tun bayan harin da wasu mutane dauke da bindigogi suka kai wa caji ofis din yan sanda a yankin, wadanda ake zaton yayan kungiyar Boko Haram ne suka kai wannan mummunan hari.
Inda suka ringa harbi cikin iska daga bisani kuma suka cinnawa wani sashi na caji ofis din wuta tare kuma da babbake motar yan sandan da ke akan titi.
Abubakar Haruna mazaunin wannan unguwa ne, kuma yace akan idanunsa wannan al'amari ya faru ya bayyana yadda wadannan mutane suka kawo farmakin. Shima wani mutum dake makobtaka da wannan wuri ya bayyana yadda suka kwana cikin firgici a sakamkon karar bindigogi da suka jiyo.
Tun adaren Talata dai sojoji suka mamaye wannan unguwa, amma kafin wayewar gari aka janyesu, lamarin da yasa mutane suka mayar da wurin da abin ya faru wurin kallo.
Anata bangaren rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar wannan hari, ta kuma kara da cewa harin ya yi sanadiyyar jikkata jami'an ta guda uku, tare da bayyana cewa za a ci gaba da bincike.
Har ila yau kuma a yammacin Talata ne masu ruwa da tsaki a jihar ta Kano, suka gabatar da wani taro a fadar gwamnatin jihar domin kamo bakin wannan matsaloli. Taron ya sami halartar Mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da gwamnan jihar Alhaji Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu tsoffin mataimakan gwamnan jihar da malamai da attajirai da sauran al'umma.
Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Usman Shehu Usman