1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Netherland ta yi murabus

Abdullahi Tanko Bala
January 15, 2021

Gwamantin Netherlands ta yi murabus sakamakon badakalar tallafin kula da yara da ya yi wa dubban iyaye rashin adalci a cewar Firaministan kasar Mark Rutte

https://p.dw.com/p/3nzVT
Niederlande Mark Rutte
Hoto: Piroschka van de Wouw/REUTERS

Matakin murabus din na zuwa ne yayin da ya rage yan makonni a gudanar da zaben majalisun dokoki da aka tsara yi a kasar a watan Maris.

Badakalar ta tozarta iyaye kimanin 20,000 wadanda bisa kuskure aka nuna su a matsayin yan damfara suna karbar kudin tallafin kula da yara wadanda kuma aka jefa su cikin matsanancin halin rayuwa na rashin kudi.

Mark Rutte yace abin takaici ne doka ta gaza kare al'umma daga karfin gwamnati.

Akwai yiwuwar murabus din gwamnatin ba zai yi tasiri ba sosai akan zaben yan majalisar dokokin da aka shiryayi  a ranar 17 ga watan Maris kasancewar jam'iyyar VVD ta firaministan ita ce a akan gaba a ra'ayin jama'a kuma yana iya kafa sabuwar gwamnati.