An rataye wadanda suka haifar da gobarar daji
October 21, 2021Gwamnatin kasar Siriya ta rataye wasu mutum ashirin da hudu (24) da aka samu da laifin hannu a haddasa gobarar daji da gangan, da ta janyo asarar rayuka da dukiya a cikin kasar a bara. Akwai karin mutum goma sha daya da aka yanke ma hukuncin daurin rai da rai baya ga wasu masu kananan shekaru da aka yanke ma hukuncin zaman gidan yari na shekaru goma da kuma ashirin.
Ma'aikatar shari'ar kasar ta ce, an dai kama mutanen bisa bayanan da aka tattaro, a yayin tuhumarsu sun amince da kunna wutar daji a watannin Satumba da Oktobar bara, baya ga kashe mutane uku, gobarar ta lakume hectocin dubu goma sha uku na gonaki da hectocin filayen noma sama da dubu sha daya baya ga lalata gidaje fiye da dari uku da hamsin. Siriya na daga tsauraran matakai kan masu yi wa kasarta zagon kasa da cin amanar kasa.
Wannan shi ne karon farko da gwamnati Shugaba Bashar al-Assad ke amincewa da zartas da hukuncin tun bayan da Kungiyar Amnesty International ta soma zargin gwamnatin da yin hakan a bara.