1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin ƙasar Potugal ta amince da a taimakawa ƙasar Girka

April 29, 2010

Ƙasar Potugal da ke cikin halin tsaka mai wuya ta amince da a taimakawa ƙasar Girka

https://p.dw.com/p/NAQv
Cavaco Silva shugaban ƙasar PotugalHoto: picture-alliance/ dpa

Gwamnatin ƙasar Potugal ta amince da a taimakawa ƙasar Girka domin ta fice daga cikin halin matsin  na tatalin arziki da ta ke ciki.Gwanatin wace za ta miƙa ƙudirin dokar amincewa da taimakawa ƙasar Girka ga majalisar dokokinta,itama da kan ta ƙasar ta Potugal da Spain suna daga cikin ƙasashen da da ke kan hanyar fuskantar irin wannan barazana.

Taimakon da ƙasar ta Potugal ta kan iya bayarwa ga na ta kaso na kuɗaɗen talafin zai iya kai miliyion 770 na kudin euro tun da farko ƙungiyar tarayya turai da hukumar tsara kudade ta duniya sun buƙaci ƙasar Girka da ta kaddamar da shirin tsuke bakin aljihun gwamnnatin a cikin shekaru biyu na farkon tsarin.

Wakilai na ƙungiyar Eu da na asusun bada lamuni na duniya AMF sun sheda cewa ƙasar ta Girka zata addana kudade kamar miliyon 25 na kudin Euro da zata samu daga cikin kuɗaɗen da za ta rage na albashin maikata dakuma karin kudaden na haraji.

Mawallafi : Abourahamane Hassane

Edita        : Mohamed Nassiru Awal