1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar ta yi bitar yarjejeniya da Amirka

February 9, 2017

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tana samun tallafi daga Amirka musamman kan fannin tsaro inda suka sake duba yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/2XFMD
Ibrahim Yacouba Außenminister Niger
Ibrahim Yacouba Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar NijarHoto: DW/A. M. Amadou

A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ce hadin gwiwa da ta Amirka sun yi wani taro na wuni daya da zummar duba halin da huldar kasashen ta ke ciki ta fannin tsaro. Nijar na daga cikin wasu kasashe 6 na Afirka da ke cin moriyar wani shiri da Amirka ta ke da shi ga kasashen don inganta tsaro abubuwan da suka ba ta damar kafa sansanonin soja da girke makamai a yunkurin Amirka na yaki da ta’addanci.

Jamhuriyar ta Nijar tana samun gajiya gami da fannin tsaro da wasu fannoni masu muhimmanci daga Amirka.