Firaministan Habasha na ziyarar aiki a Afirka ta Kudu
January 12, 2020Talla
Firaminista Ahmed na Habasha din ya mika wannan bukata ce yayin da yake ziyarar aiki a kasar Afrika ta Kudu a wannan Lahadin, ya kuma kara jaddada muhimmancin shigar Afirka ta Kudu cikin batun a daidai lokacin da ake dab da nada sabon shugabancin kungiyar AU.
Tsamin dangantakar Habasha da Masar dai ya samo asali ne a shekara ta 2011, bayan gwamnatin Habasha ta kaddamar da shirin samar da wata cibiyar ruwa domin samar da hasken wutar lantarki irin sa na farko a nahiyar Afrika. Al'amarin da ya sanya mahukuntan Masar zargin Habasha da yunkurin haifar da koma baya a harkokin samar da wadataccen ruwa a fadin kasar.