Hada-hadar Kirsmeti a lokacin corona
Bisa al'ada watannin Nuwamba da Disamba na zama mafi bunkasar ciniki ga kantuna da shaguna. Amma matakan kulle saboda corona sun janyo koma baya. Annobar ta shafi hada-hadar kasuwanci a Kirsmetin bana.
Koma baya a ciniki saboda corona?
Kirmetti na karatowa hakazalika lokacin hada-hadar kasuwanci, sai dai dokar kulle ta yi babban tasiri ga yadda Jamusawa ke gudanar da kasuwanci. Matakin rufe shaguna a Jamus a Kirsmetin bana ya shafi kasuwanci, wanda haka ya sa ciniki a lokacin bikin na bana ya yi rauni idan aka kwatanta da na bara. Tuni dai kantuna da shaguna suka tabka asara babba.
Ba a iya shiga gari don sayayya
Ba za a ga jama'a a cikin gari a lokacin shirye-shirye da hada-hadar Kirsmetti bana ba, saboda dokar kulle da mahukuntan Jamus suka kafa. Jama'a ba za su iya sayen kayan Kirsmeti a cikin gari ba. Sun koma ga yi ta yanar gizo. Ga masu kantuna da shaguna wannan yanayin ba mai dadi ba ne, domin hada-hadar kasuwanci a lokacin Kirsmetti ta fi sama musu kudin shiga.
Ciniki ta intanet ya samu tagomashi
Sakamakon annobar corona, harkar kasuwanci ta intanet ta bunkasa sosai. A lokacin shirye-shiryen Kirsmeti ma harkar za ta ci gaba da bunkasa, za kuma ta zama abin farin ciki ga wannan bangare. Kungiyar 'yan kasuwa ta ce kasuwanci ta intanet zai karu da kashi 12 cikin 100 a wannan Kirsmeti, wanda ya yi daidai da Euro miliyan dubu 17 a hada-hadar cinikin ta Kirsmeti.
Boca ke kan gaba
Shin a bana me ake ajiyewa karkashin bishiyar Kirsmetti a Jamus? A nan ma kungiyar 'yan kasuwar Jamus ta yi hasashe. A sahun gaba: Boca ko Voucher. Yadda boca ke ba da damar zabi da yawa ya sa tana da farin jini ko a lokuta na rikici da rashin tabbas. An yi hasashe kashi 30 cikin 100 na Jamusawa za su samu bocarsu karkashin bishiyar Kirsmeti.
Sahu na biyu: Kayan wasan yara
Hada-hadar sayen kayan wasan yara ita ce a sahu na biyu a jerin kayayyakin da ke samun tagomashi suke kuma jan hankali na kyaututtuka. Yara dai na maraba da irin kyaututtukan kayan wasa da suke samu a lokacin bikin na Kirsmeti.
Litattafai da kayan rubutu
Sahu na uku shi ne litattafai da kayan rubutu, da ke zama abin jan hankali na kyaututtuka. A cikin wannan rukuni ma kusan kowa zai samu rabonsa. Bisa hasashen kungiyar ciniki ta Jamus kashi 26 cikin 100 na Jamusawa za su samu kyautar littafi ko abin rubutu ko sauran kayan rubutu karkashin bishiyar Kirsmeti.
Kayan kwalliya da kayan gyaran jiki a sahu na hudu
Daga ruwan sabulun wanka zuwa man shafawa har su jan baki da kyallen rufe fuska: Kashi 20 cikin 100 na Jamusawa za su yi murna da kayan kwalliya da na gyaran jiki a lokacin bikin. Za su iya yin tsada, a takaice a bana masu amfani da kaya za su kashe Euro 330 wajen sayen kayan kyauta a cewar masu nazarin harkokin kasuwanci na GfK.
Tsabar kudi karkashin bishiya
Za a ajiye tsabar kudi karkashin bishiyar Kirsmeti. Kimanin kashi 19 cikin 100 na Jamusawa za su yi farin ciki da wannan. Saboda yana a sahu na biyar a cikin kyaututtuka da aka fi so. A binciken jin ra'ayin jama'a da kungiyar ciniki ta yi a dukkan bangarorin ta gano irin kayayyakin kyauta da al'umma ke so. Daga cikin 10 da aka fi so har da tufafi da kayan abinci da kayan ado.
Hattara wajen sayen kaya ta intanet!
Musamman ya kamata a yi hattara da sayen kayan lanturoni ta intanet. Hukumar kula da wayoyi ta tarayyar ta yi gargadi game da kaya masu hadari musamman daga kasashen Asiya, da sau da yawa ba sa cika ka'idojin ingancin kaya kamar yadda doka ta tanada. A wasu lokutan ana samu hadura masu barazana ga lafiya. Za a iya kare kai idan aka saye daga amintattun kamfanoni masu kuma gaskiya.