Hada-hadar 'yan wasa mafi tsada a Bundesliga
Dan wasan tsakiya na kungiyar RB Leipzig Josko Gvardiol zai koma Manchester City, kungiyar zakarun Premier League. Yana daga cikin 'yan wasan Bundesliga mafi tsada kawo yau.
10. Dominik Szoboszlai - Euro miliyan 70
Mai shekaru 22, kwararren dan wasan zai bar kungiyar zakarun kwallon kafar Jamus RB Leipzig zuwa Liverpool a lokacinn bazara a 2023. Mai horar da 'yan wasan Jürgen Klopp ya bayyana komawar dan wasan dan kasar Hungary da cewa ya zama wajibi domin dorewar makomar kungiyar a yanzu da kuma nan gaba. An yi musayar Szoboszlai daga RB Salzburg zuwa RB Leipzig a 2021 a kan kudi yuro miliyan 36.
9. Naby Keita - Euro miliyan 70
Shahararren dan wasan RB Leipzig ya sauya sheka zuwa kungiyar Liverpool bayan jinkiri a kakar 2018. An sanar da sauyin tsawon lokaci kafin nan. An yi musayar dan wasan a kan kudi yuro miliyan 70
8. Kevin De Bruyne - Euro miliyan 74
Sai bayan wasanni na lale kati da darajar Bundesliga a wancan lokaci, dan wasan ya sanya hannu a kan kwantaragi da Manchester City a kan kudi yuro miliyan 74 a 2015. Kodayake kungiyar ta sami karin tagomashin kudi wajen musayar tasirin wasan De Bruyne na raguwa.
7. Erling Haaland - Euro Miliyan 75
Kungiyar BVB ta sanya yuro miliyan 75 a matsayin kudin musayar dan wasan mai shekaru 21 dan kasar Norwaya a kwantaragin yarjejeniya. Manchester City ta biya kudin a kakakr 2022 a kan Haarland wanda aka dauka dan wasan gaba mafi kwarewa a duniya. Wajen biyan albashinsa, sai Premier League ta zura hannu sosai cikin lalita, ana maganar yuro miliyan 30 a duk shekara.
6. Lucas Hernandez - Euro Miliyan 80
Shi ne dan wasa mafi tsada da kungiya FC Bayern Munchen ta sayo: Lucas Hernandez, wanda ya zama zakaran duniya da Faransa a 2018 ya koma Munich daga Atletico Madrid a kakar 2019 a kan kudi yuro miliyan 80 a matsayin dan wasa mafi tsada da aka sayo a tarihin Bundesliga a wancan lokaci kuma mai tsaron baya mafi tsada a duniya.
5. Jadon Sancho - Euro Miliyan 85
Dan wasan kasa na Ingila mai shekaru a 21 a wancan lokaci, Jadon Sancho ya bar Borrusia Dortmund zuwa Manchester United a gasar Premier a kakar 2021 a kan kudi yuro miliyan 85. Ciniki mai armashi ga BVB, shekaru hudu kafin nan BVB ta sayo matashin dan wasan mai kwazo daga Manchester City a kan kudi yuro miliyan bakwai da rabi.
4. Josko Gvardiol - Euro Miliyan 91,5
Jigo ne na 'yan wasan tsakiya, amma kwallo daya ta sa dan kasar Croatian ya zama dan wasa na gaban goshi a wajen Pep Guardiola. Kwallo daya (1) da Gvardiol ya ciwo wa RB Leipzig a watan Fabrairun 2023 a gasar zakarun turai da ya sami nasara a kan Manchester City.Watanni shida bayan nan zakarun turan suka sayi dan wasan da ya zama mafi tsada a duniya.
3. Kai Havertz - Har zuwa Euro Miliyan 100
A kakar 2020 ba tare da bata lokaci ba Chelsea ta biya yuro miliyan 80 kan dan wasan Kai Havertz mai shekaru 21 a wancan lokaci ga Bayer 04 Leverkusen wanda zai karu har zuwa yuro miliyan 100 ta hanyar kwazo da karin kudi na bonus. Musayar ga Leverkusen kwalliya ta biya kudin sabulu.
2. Jude Bellingham - Euro Miliyan 103
Bayan shekaru uku a Borrusia Dortmund dan kasarta ta Ingila zai koma Real Madrid a kakar 2023 inda zai sanya hannu a kan kwantaragi da "Royals" har zuwa 2029. Kudin musayar, wani kaso daga ciki zai je ga kungiyar da ya sami horo Birmingham City. A yarjejeniyar, darajar dan wasan na iya kaiwa yuro miliyan 133.9
1. Ousmane Dembélé - Euro miliyan 105
Kungiyar Barcelona ta biya yuro miliyan 105 ga Borrusia Dortmund domin musayar Dambele a kakar 2017, sai dai sakamakon nakasu da raunuka darajarsa ta yi kasa.