Hadarin jirgin sama na sojoji a Aljeriya
April 11, 2018Jirgin ya fadi ne jim kadan bayan tashin sa daga filin tashi da saukar jiragen sama na sojoji na Boufarik da ke da nisan kimanin kilomita 30 daga Algiers babban birnin kasar ta Aljeriya. Ministan tsaron kasar ta Aljeriya da ya tabbatar da afkuwar hadarin, ya shaidawa manema labarai cewa, mutanen da suka mutu sun hada da ma'aikatan jirgin guda 10 da kuma fasinjoji 247 wadanda akasarin su sojojin kasar ne da iyalansu.
Jirgin ya tashi ne daga Boufarik zuwa Tinduf da kuma Beshar, inda Tindouf din ke da nisan kilomita dubu daya da 800 da birnin Algiers kana yana kusa da kan iyakar Aljeriyan da kasar Marokko, yayin da Bechar ke da nisan kilomita 1000 da Kudu maso Yammacin kasar, kuma nan ne ma ake da wani babban barakin sojojin kasar ta Aljeriya.