1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgin yakin Yuganda ya yi sanadiyyar rayuka

Zainab Mohammed Abubakar
January 3, 2024

Wani jirgin soji a Yuganda, wanda ake amfani da shi wajen yaki da masu tsattsauran ra'ayi mna ADF a Kwango da ke makwabtaka ya fada kan wani gida.

https://p.dw.com/p/4aqEh
Hoto: Alain Uaykani/Xinhua/picture alliance

Har yanzu dai babu masaniya dangane da abun da ya janyo hadarin jirgin a gundumar Ntoroko da ke kan iyakar Kwango, sai dai kakakin rundunar sojin Yugandan Felix Kulayigye ya danganta da rashin kyawun yanayi.

A shekarun baya bayan nan dai, jiragen sojojin Yuganda da dama sun sha yin hatsari da ake dangantawa da yanayi.

Ko a cikin watan Satumba 2022, hatsarin jiragen sojin biyu da ake amfani da su wajen yakar ADF sun fado a gabashin kasar Kwango, tare da halaka sojojin Yugandan 22.