Mutane sun mutu a hadarin mota
November 12, 2022Talla
Wata motar safa da ta yi hadari a yankin arewacin Masar ta zama sanadiyar mutuwar mutane 19 a wannan Asabar. Jami'an agaji sun ce hadarin da ya auku a yankin kogin Nuli ya kuma raunata mutane shida da ke samun kulawar likita.
Kimanin mutane 7000 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon haduran motoci a kasar masar a shekarar 2021, duk da yake Masar na zama kasa mafi yawan al'umma a daukacin kasaashen yankin Larabawa. Ana zargin lalacewar hanyoyi a cikin wasu dalilan da ke haddasa yawan hadurran motocin da sauran ababen hawa a kasar Masar.