Kungiyar NATO EU sun sanar da hadakar tsaro
January 11, 2023Talla
Matakin na zuwa ne bayan wani hari da aka kai kan bututun iskar gas na karkashin ruwa na Nord Stream a bara da kuma yadda kungiyoyin biyu ke neman karfafa hadin gwiwa a sakamakon mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.
Shugabar hukumar gudanarwa ta tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce rundunar za ta hada kwararru na EU da NATO don yin nazari kan raunin muhimman wuraren, tare da ba da shawarar hanyoyin da za a kare su.
A wata ganawa da babban sakataren kungiyar NATO Jens Stoltenberg a Brussels na Belgium, von der Leyern ta ce sun ga irin zagon kasa da aka yi a kan Nord Stream, wanda ya nuna cewa akwai bukatar kasancewa cikin shirin ko ta kwana na tunkarar wannan sabuwar barazana.