Janar Haftar ya kai ziyara a fadar Abdel Fattah al-Sissi
April 15, 2019Kwanaki goma da fara kai hare-haren kwace birnin Tripoli a hannun gwamnatin hadin kan kasa mai goyon bayan kasashen duniya, Khalifa Haftar babban kwamandan sojin ‘yan tawayen Libiya ya gana da Shugaba Abdel Fattah al-Sissi na kasar Masar a daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da matsin lamba ga Khalifa Haftar don sojan da ke masa biyayya su dakatar da hare-hare a birnin Tripoli.
Shugaba Abdel Fattah al-Sissi ya gana da Janar Haftar yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa hare-haren soja kan Tripoli ya haddasa hasarar rayukkan jama’a 120 tare da jikkata akalla mutane 600. Duk da kiraye-kirayen kasashen duniya Shugaba Abdel Fattah al-Sissi da Janar Khalifa Haftar na da ra’ayi daya game da batun warware rikicin kasar Libiya inda suke cewa dole ne a yi amfani da karfin soja mai makon hawa kan teburin sulhu da wadanda har gobe suke kira da cewa ‘yan ta’adda.
Kwanaki uku kafin sojan da ke biyeyya ga Janar Haftar su fara kai hare-hare a Tripoli sai da madugun ‘yan tawayen ya yi wata ganawa da Sarki Salman na Saudiyya lamarin da ya haifar da zarge-zargen cewa Saudiya na da hannu a cikin rikicin. Gwamnatin rikon kwarya mai goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga ga kwamitin sulhu na Majalaisar Dinkin Duniya da ya dauki matakan da suka dace domin dakile yunkurin Khalifa Haftar na jefa kasar cikin mawuyacin hali.