Hajjin 2020: Alhazai 10.000 sun isa birnin Makka
Maniyyata kimanin 10.000 ne suka isa birnin Makka domin gudanar da aikin hajjin bana, sabanin miliyoyin Musulmi da suka saba gudanar da wannan ibada. Mahukuntan sun tsaurara matakan tsaro da na kariya daga COVID-19.
Yadda aka kammala tsaftace harami
Gabanin aikin hajjin bana, ma'aikata da ke dawainiyar tsaftace Masallacin, sun samu karin aiki na tsara yadda mahajjata za su gudanar da ibada cikin matakan hana yaduwar cutar coronavirus da mahukunta suka tanadar, musanman saka tazara a tsakanin juna. Akwai shaidar da ke nuna tazarar da za bayar tsakanin mutane da kuma layin da alhazai za su bi, yayin gudanar da dawafi a Masallacin mai tsarki.
Dokar bayar da tazara
A can baya, dubun-dubatar mutane ke gudanar da aikin hajjin, sabanin 10.000 kacal da za su sauke faralin a bana. Wannan ya bai wa mahukunta damar tsara ayyukan ibadar ba tare da wata matsala ba. An zabi maniyyatan ta kafar Internet, kafin daga bisani aka soma tantance lafiyarsu ta hanyar gwajin zafin jiki a yayin da suka isa birnin Makka. Daga karshe kuma aka killacesu tsawon makonni biyu.
Bin doka
An shawarci mahajjatan da su kiyaye dokokin da aka gindaya yayin gudanar da aikin hajjin, ana son su saka tazarar kimanin kafa biyar a tsakanin juna yayin da suke dawafi. Haka kuma ba a yadda su dafa ko al'adar nan ta shan nono a dakin Ka'abar ba, kamar yadda aka saba yi a can baya ba.
Sanya takunkumin kare fuska
Jami'ai sanye da takunkumin fuska domin gwadawa alhazai mahimancinsa. Akasarin mahajjatan bana, 'yan asalin kasar Saudiyya ne sai kuma 'yan kasashen waje da ke zaune a cikin kasar. Tuni aka kulle filin sauka da tashin jiragen sama na kasar. Mutane sama da dubu 270 ne cutar corona ta kama a kasar, a yayin da ake samun sababbin alkaluma na masu dauke da ita tsakanin 3000 zuwa 4000 kusan kullum.
Sau daya a rayuwa
Ana son Musulmin da ya samu dama, ya gudanar da aikin hajji koda sau guda ne a rayuwarsa, muddin yana da koshin lafiya kuma ya balaga tare da arzikin yin hakan, kamar yadda ya ke a cikin littafin Alkura'ani mai tsarki a Surah ta uku aya ta 97. Hajji na daya daga cikin shikashikan Musulumci.
Tsaftace duwatsun jifan shedan
Al'adar jifan shedan da ake yi a Mina kusa da birnin Makka, na daya daga cikin ayyukan hajjin. A nan ma an shawarci mahajjatan da su bayar da tazara, an kuma tanadi duwatsun da za a yi jifan shedan da su. Duwatsun da dardumar yin Sallah, duk an tsaftace su ta hanyar wankesu da maganin kashe kwayoyin cuta.
Waiwaye adon tafiya
A shekarar 2018, alhazai sama da miliyan biyu ne suka gudanar da aikin hajjin, kamar yadda ake gani a wannan hoton. Alhazan kenan da suka taso daga birnin Makka kan hanyarsu ta zuwa Mina. Baya ga cewa aikin hajjin ibada ne, yana samar wa Saudiyya kudadden shiga. An kimanta cewa, kimanin Euro biliyan 10 kwatankwacin sama da dalar Amirka biliyan 11, kasar ke samu yayin aikin hajjin kowace shekara.