1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da a ke ciki a gabas ta tsakiya

Yahouza S.MadobiJuly 22, 2006

A na ci gaba da ɓrin wuta tsakanin Isra´ila da Hezbollah a kudancin Labanon

https://p.dw.com/p/Btyv
Hoto: AP

Dakarun Isra´sila da na Hezbollah sun yi ɓarin wuta a kwana na 11 ga ɓarkewar saban yaƙi tsakani su.

Bayan hare haren ta sararin samaniya da Isra´ila ke ci gaba da kaiwa a Lababon , rundunonin 2 sun gwabza faɗa, ta ƙasa a kudancin Labanon.

A harin da ta kai da yau assabar, Isra´ila ta yi kaca kaca, da dogayen ƙarafunnan Labanon, masu jona wayar sadarwa ta sallular tafi da gidan ka, da kuma tashoshin Radio da na Telbajan.

Sannan rundunar ta yanke shawara yin shigar Ƙundunddune cikin Labanon, domin fuskantar gaba da gaba, mayaƙan Hezbollah.

Rundunar Tsahal ta Isra´ila, ta yi ruwan takardu, wanda ke ɗauke da kira ga al´ummomin kudancin Labanon,su ka ƙauracewa wannan yanki, da ke shirin fuskantar amen wuta, ta sama daga Isra´ila.

Dakarun na Isra´ila sun bayana ɓankaɗo maɓuyar rokokin Hezbollah a garin Maroum Al Ras.

Isra´ila ta ce ta ragargaza a ƙalla kashi 50 bisa 100 na makaman Hezbolllah, labarin da, ba da wata wata ba, yan Hezbollah su ka ƙaryata.

Sun bada cikkakar shaida, tare da harba rokoki fiye da 70 a arewancin Isra´ila.

Isra´ial ta amsa kiran da ƙasashen dunia ke mata na buɗa wata turba domin kai agaji abinci, da jigillar yan gudun hijira.

Saidai, Isra´ilwa sun ce, za a gudanar da aikin agajin tare da sa idon su.

Ta fuskar diplomatia, ƙasashe da ƙungiyoyi danan-daban na dunia, na ci gaba da huruci, a kan wannan yaƙi wanda ya zuwa ya hadasa mutuwar mutane a kala 500.

Ministan harakokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ,da ya zai ziyara aiki a gabas ta tsakiya, ya bayana wajibcin ɗaukar matakan dakatar da wannan bila´i.

Shima ministan harakokin wajen France Philip Douste Blazy a yau, ya kammala ziyara a wannan yanki, inda ya yi kira ga ɓangarorin 2 su tsagaita wuta.

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, ta nunar da cewa, batun tsagaita wuta, da yan ta´ada, bai taso ba .

Gwamnatin Amurika ta ƙara ƙarfin gwiwa, ga Isra´ila, ta ci gaba da kai hare haren, har lokacin da ta gurfanar Hezollah.

Ya zuwa yanzu gwamnatin Labanon, ta bakin shugaban ƙasa Emil Lahud na ci gaba da kira ga kasashen ƙetare da su taimakawa Labanon ta fita daga wannan ƙangi.

Al´ummomin Labanon za su ci gabada zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya,dukkan wannan fitina ba zata raba kawunanan su ba.

A halin da ake ciki kasashen dabandaban na turai da Amurika na ci gaba da jiggilar al´ummomin da ke Labanon.