Halin da ake ciki a siyasar Pakistan
November 26, 2007Dubban magoya bayan Nawaz Sharif sunyi dafifi domin yi masa maraba, jim kadan da komowar Pakistan, bayan yayi zaman neman mafakar siyasa a Saudiyya, sanadiyyar juyin mulki da shugaban Pakistan Pervez Musharraf yayi masa a 1999.
To amma menene haka kwatsam sai ka komo gida ba shiri, tambayar kenan da manema labarai suka yi wa Nawaz Sharif sai ya amsa da cewar.“ Na zo ne don na bada tawa gudummawar wajen gina dimukradiyya a kasa ta,kuma na ceto ta daga hanun yan mulkin kama karya, kazalika zanyi kokari wajen fitar da kasar daga halin rudu data sami kanta ciki a shekaru 8 da suka gabata “
Tun shigowar Nawaz Sharif jiya daga kasar Saudiyya siyasar Pakistan ta kuma daukan dumi,don kuwa a zance nan da ake tsohon Firaministan na Pakistan ya fito fili ya karyata masu tunani cewar ko wata kila akwai wani shiri tsakaninsa da gwamnatin kasar Saudiyya, ko kuma shugaban Pakistan Pervez Musharra kan yadda zasu gudanar da mulki tare da Musharraf, inda yace shi ba zai nemi wani mukami ba a karkashin gomnatin Musharraf don kuwa ba halartaciya bace.
To amma wata majiyar ta ruwaito cewar muddin in hadin kai bai samu ba daga bangaren Nawaz Sharif ga gwamnatin Musharraf,to lamarin ka iya tada tsohon likin dake akwai kan tsohon Firaministan, don tuni har Atoni janar na Pakistan Malik Qayyum, ya soma hasashe cewar ba zai yiwu ba tsohon Firamnistan ya tsaya takara, sabili da hukuncin dake kansa na daurin rai da rai a gidan fursuna,wanda gwamnatin Pervez Musharraf ta zatas kansa bayan tayi masa juyin mulki a 1999.
Yanzu dai babu wanda zai iya yanke hukunci kan ko Nawaz Sharif zai bada kai bori ya hau wa gwamnatin Musharraf ko akasin haka, don wata majiyar ta ruwaito Mr. Sharif wanda ya rike mukamin Firaminista a Pakistan har sau biyu yana mai bayyana cewar kafin ya tabbatar da wannan matsayi daya dauka sai ya gana da jama’iyyar sa tukuna,to amma wani rahoton ya nunar da cewar jama’iyyar Nawaz Sharif tana jira ne ta ga irin matsayar da jama’iyyar Benazir ta (PPP)zata dauka game da zaben kafin ta bayyana nata matsayar a bisani.
To amma a zancen nan da ake tuni har Bhutto ta rigaya ta rigaya ta mika nata takardar don tsayawa takara a zaben na ranar takwas ga watan janairu mai zuwa.
A wani bangare kuwa, yanzu duk bai shige sa’i 48 ba nan gaba shugaba Musharraf ya dauki rantsuwar aiki a matsayin shugaban Pakistan na farar hula, bayan ya tube kakin sa na soja. Kuma zai mika wa mataimakinsa Janar Ashfaq Pervaiz Kiyani ne mukaminsa na babban hafsan hafsoshin kasar a ranar Alhamis, 28 ga wannan wata, mukamin da tun hasali Nawaz Sharif ne ya nadda Musharraf kai a cikin watan Oktoban 1998, bayan tsohon babban hafsan kasar Pakistan a wancan lokacin Janar Jehangir Karamat yayi murabus.
Musharraf du da cewar zai sauka daga kan wannan mukami, zai cigaba da samun kariya ne daga wani mai mukamin birgadiya janar na sojin kasar matsayin sa na shugaban gwamnatin farar hula, har zuwa karshen wa’adin wasu shekarun.