Harkokin ilimi a Najeriya da Nijar
September 16, 2021Talla
Sau da dama, ana fuskantar kalubale a fannin ilimi musamman a kasashe masu tasowa. A Jamhuriyar Nijar da Tarayyar Najeriya, matsalolin tsaro na taimakawa wajen samun koma baya a fannin ilimi musamman na makarantun firamare da sakandare. A baya-bayan nan dai, ana ta kwashe daliban makarantun firamare da sakandare har ma da jami'o'i a jihohin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
A baya ma dai an samu irin wannan matsalar a yankin Arewa maso Gabashin kasar daga 'yan ta'adxdan Boko Haram, sai dai lamarin ya fi kamari a yanzu haka a yankin Arewa maso Yamman da 'yan bindiga suka taso gaba. Ana dai alakanta wadannan matsaloli da yawan faduwar jarrabawa da ake samu daga dalibai, musamman jarrabawar kammala sakandare da ta shiga jami'a.