Halin da mai murabus na Libya ke ciki a London
March 31, 2011Hukumomin Birtaniya sun titsiye ministan harkokin wajen Libya da ya yi murabus wato Moussa Koussa, tare da yi masa tambayoyi game da dalilansa na raba gari da gwamnatin Moammar kadhafi. Ministan da ke zama na hannun dama shugaban Libya ya sauka daga muƙaminsa ba zato ba tsammani, tare da dira birnin London a larabar da ta gabata domin neman mafaka. Ministan harkokin wajen ƙasar Birtaniya William Hague, yace saukar Koussa wani babban giɓi ne ga shugaba Khaddafi na ƙasar Libya da tushen mulkinsa ke tangal tangal.
Sai dai kuma sojojin dake biyayya ga shugaba Khaddafi sun ci gaba da fatattakar 'yan tawaye, tare da karɓe garin Ras- lanuf mai arzikin man fetur daga hannunsu. Wannan asarar da 'yan tayar da ƙayar baya ke fuskanta ya faru ne, kwanaki 10 bayan da sojojin taron dangi suka ƙaddamar da luguden wuta akan sojojin Ghaddafi da sunan kare fararen hula. Awani ci gaban kuma sakatare janar ƙungiyar tsaro ta NATO wato Anders Fogh Rasmussen yace ƙungiyar ta karɓi ragamar aiwatar da ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya da ya tanadi amfani da hanyoyin daban daban domin ja wa kadhafi birki a yunƙurin murkushe boren ƙin jinin gwamnatinsa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal