1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

210116 Tunesien Unruhen

Borchers, Jens / Rabat/ Lateefa/YBJanuary 22, 2016

Ana ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Tunusiya a kai a kai sakamakon matsalar rashin aikin yi ga matasan kasar.

https://p.dw.com/p/1HibA
Tunesien Proteste in Tunis
Masu zanga-zanga a birnin TunisHoto: Reuters/Z. Souissi

A jihar Kasserine da ke gab da kan iyakar kasar da Aljeriya an yi wata taho mu gama tsakanin jami'an 'yan sanda da masu zanga-zangar a inda rahotanni suka tabbatar da asarar rayukan mutane yayin da wasu da da ma suka jikkata. A sauran jihohin kasar ta Tunusiya ma dai ana ci gaba da zanga-zanga ta kin jinin gwamnati da ma zargin cin hanci da karbar rashawa. Gwamnati dai a hannu guda na kokarin kwantar da hankula ta hanyar yin sababbin alkawura.

Jihar Kasserine dai na tsakiyar kasar ta Tunusiya kana tana da yawan mutane 80.000, kuma kaso 30 cikin 100 na mazauna wannan jiha na fama da rashin aikin yi da matsanancin talauci. Tsahon kwanaki ke nan matasan wannan jiha ke gudanar da zanga-zanga, inda kuma suke samun arangama tsakaninsu da jami'an 'yan sanda da ke son murkushe zanga-zangar da karfin tuwo.

Ga dai ta bakin guda daga cikin masu zanga-zangar da ke cikin bacin rai wanda ya bayyana dalilansu na fitowa kan tituna:

Demonstration in Bourguiba avenue
Matasa masu zanga-zanga a Bourguiba avenueHoto: Taib Kadri

"Dukkanmu ba mu da aikin yi, baki dayan mutanen da ke nan wajen ba su da aiki yi. Ba mu da kudin da zamu sayi na sawa a bakin salati, 'yan siyasa na yakar junansu ne kawai, shi ne abin da yake faruwa a nan wajen."

Zanga-zangar ta baya-bayan nan dai ta barke ne biyo bayan mutuwar wani matashi, matashin na daya daga cikin wadanda aka dauki sunayensu za a basu aiki, sai dai matsalar cin hanci ta hana a dauke shi aikin, abin kuma da ya janyo matashin ya hau kan falwaya a gaban ofishin gwamnan jihar ta Kasserine har wutar lantarki ta ja shi ya ce ga garinku nan.

A yammacin Larabar nan ma wani dan sanda mai kimanin shekaru 25 ya rasa ransa a wani dan karamin gari kusa da jihar Kasserine, har yanzu ba a gano musabbabain mutuwarsa ba.

Har ila yau a bayyane ta ke gwamnatin ta Tunusiya na cikin tsaka mai wuya, akwai rikicin cikin gida a jam'iyya mai mulki, kana an rusa majalisar zartaswar kasar.

Proteste in Kasserine Tunesien
Matasa masu zanga-zanga a garin KasserineHoto: picture-alliance/AA

Shima a nasa bangaren shugaban kasar ta Tunusiya Beji Caid Essebsi ya bayyana cewa lamarin na da tsauri kana ba za a iya shawo kan dukkan matsalolin nan take ba.

"Mun tsinci kanmu cikin wani hali mai tsanani. A Tunusiya akwai mutane 700.000 wadanda basu da aikin yi. 250,000 daga cikinsu sun kammala karatunsu na difloma. Akwai yankunan da ke fama da talauci. Akwai yankunan da ke fama da matsanancin talauci, ya zamo wajibi Turai da ke zaman abokiyar huldarmu ta taimaka mana".

A na dai ci gaba da zanga-zanga a jihohi irin su Thala da Sousse, da ma gudanar da wata kwarya-kwayar zanga-zanga a Tunis babban birnin kasar.