1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin samun mafita ga fararan hull a Aleppo

Salissou Boukari
December 14, 2016

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai kira takwaransa na Rasha Vladimir Putin domin ganin an samu yin biyayya ga yarjejeniyar tsagaita buda wuta a birnin Aleppo.

https://p.dw.com/p/2UG8z
Syrien Stadtpanorama Aleppo 2006
Hoto: Getty Images/AFP/R. Haidar

Bayan wata 'yar lafawa da aka samu ta tsawon awoyi 15, dan karamin yankin da ya rage wa 'yan tawayen na Aleppo ya fuskanci ruwan manyan makamai daga sojojin gwamnatin Siriya da masu mara musu baya, kafin daga bisani jiragen yakin kasar su shiga yin nasu ruwan bama-baman a cewar kungiyar da ke kula da sa ido kan hakkokin bil-Adama a kasar ta Siriya.

Da yammacin ranar Talata ce dai kasashen Rasha da Turkiyya suka sanar da cimma yarjejeniyar dakatar da buda wuta tare da 'yan tawayen na Aleppo domin ganin an samu fitar da fararan hula da ma mayakan 'yan tawayen daga wannan yanki. Sannan kuma shugaban na Turkiyya ya soki Majalisar Dinkin Duniya da cewa ta kasa samar da wurare masu tsaro domin tsugunar da 'yan gudun hijiran na Siriya.