Halin tsaka mai wuya a rikicin kasar Sudan
April 20, 2023Yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin gwamnatin rikon kwaryar kasar da dakarun RSF da ke karkashin Mohamed Hamdane Daglo, kiraye-kirayen kasashe kungiyoyi na duniya sun kasa yin katabus, fadan da masharhanta ke alakantawa da rikicin cikin gida.
Ganin yadda kokarin shiga tsakani ya ci tura, wasu masana na nuna wasu kasashe da dan yantsa da suke kallo a matsayin masu kara rura wutar rikici da ke kara daukar dumi. A cikin jerin kasashen har da Masar wacce ke da alaka ta kut-da-kut da Janar Abdel Fattah al-Burhane da ma kuma karin wasu kasashe.
Masharhantan na da yakinin cewa da akwai kasashen da ke kara iza wutar rikicin kawai saboda cimma biyan bukatunsu a kan Sudan. Ko da dai alamu na nuna kasashen Saudiyya da Hadadiyar Daular Larabawa a matsayin kasashen da ke dafa wa wannan ko waccan bangare a rikicin. Amma masani Roland Marchal na mai cewa kasar Masar ta fito a fili ta nuna kyakyawar alakar da ke tsakanin Abdel Fattah al-Burhane da fadar Alkahira.
Muna da cikakkun hujjoji da ke tabbatar mana da hakan, idan muka fara da batun sojojin Masar da aka tsare a filin jirgin saman soji na Meroe. Sannan kuma da akwai jirage mallakar Masar da aka lalata tun barkewar rikicin, sai kuma shaidu da ke geremu a kan cewa an yi amfani da ko da daya ne daga cikin jiragen yakin Masar wajen yin ruwan bama-bamai a sansanin dakarun RSF da ke kusa da filin jirgin Khartoum''.
To sai dai wannan ra'ayi ya ci karo da na Mariana Peter, shugabar wani tsari da ya hada Sudan da Sudan ta Kudu wacce ke ganin babu kura ko kadan a rawar da Masar ke takawa a cikin rikicin da kawo yanzu ake fargabar ya jefa Sudan cikin yakin basasa.
Sai dai a kan wannan gaba masani Roland Marchal na da ja, domin a mahangarsa har yanzu Rasha ba ta nuna a zahiri ga bangarenta ba, sannan kuma duk da cewa Rashar da Saudiyya da Hadaddar Daular Larabawa ba sa rasa bangaren da suke mara wa baya a fakaice, to amma ya kawar da maganar cewa wadannan kasashe uku za su shiga yakin gadan-gadan domin a cewarsa kasashen na da muradu daban-daban a kan Sudan din.
A daya gefe kuma Roland Machal ya fit da maganar da ke cikin duhu kan karfin dakarun RSF abin da ya bayyana a matsayin aikin sojin haya da dakarun ke yi a Yemen karkashin Haddadiyar Daular Larabawa da kuma Libiya karkashin janar Halifa Haftar.
Rikicin dai ya kai kasar Tchadi da ke zama aminiya kuma makwabciya da ke raba iyaka ta kilomita sama da 1.000 da Sudan din ga rufe iyokokinta don kadda shafi ta shafeta, bayan da ta sanar cewa a jiya kimanin sojojin Sudan din guda 320 da suka yi ta ransu bayan barkewar rikici sun mika kansu ga sojojin Tchadin.