Halinda ake ciki a kasar Pakistan
August 10, 2007Musharraf dai ya kawo karshen waddanna rade radi inda ya sanarda cewa babu wannan doka haka shima Mujahid Hussein janar sakatare na jamiyar PML ya kara jaddada hakan ga manema labarai.
Ya kuma ce babu wani hadari na kafuwarta.
babu wani hadari na kafa dokar t abaci,babu kuma yiwuwar hakan nan gaba,idan kuma hakan ya faru wanda Allah ya hana,to ken an wasu ne suke baiwa shugaban kasar shawarar kuma ni a ganina wanda duk ya bashi wannan shawara ba aboki ne ba gareshi.
Masu lura da alamura dai suna ganin kafa dokar tabaci a kasar kamar makami ne da zai mikawa abokan adawarsa na siyasa,kuma suna ganin yin hakan zai kara baiwa abokan adawa karfi su samu nasara kansa.
Sai dai kuma tsohon shugaban hukumar liken asiri ta kasar wadda ake tsronta Hamid Gul yana ganin cewa cewa yan siyasa ne suka fara yada wannan jita jita domin wata manufa tasu.
.A ganina yan siyasa ne suka fara wannan jita jita,dom suna son biyan wata bukata tasu kuma suna son tabbatar da irin iko da suke da shi a kasar,hakazalika tare da jaddada matsayinsu a harkokin siyasarta.
Shugaba Musharraf dai ya mulki kasar ta Pakistan ba tare da wani kalubale mai karfi daga yan adawa ba,har sai bayan dakatar dab ban jojin kasar wanda ya haddasa tashe tashen hankula da adawa tukuna.
Yan adawa da masu lura da aamuran kasar sunce daya daga cikin dalilan da suka sanya ya duba yiwuwar kafa dokar t abaci shine domin rage tasirin kotunan kasar da ake ganin sun kara samun karfin iko bayan sake mayarda babban alkalin kasar Choudry.
Sai dai kuma tsohon shugaban hukumar ta leken asiri Hamid Gul yace rashin kafa wannan doka ya baiwa yan siyasa da kotuanan dama kasar Amurka da take ziga shi kunya .
O TON.ina ganin ya lalata masu shiri,dama abinda suke nema shine yamutsa kasar,domin sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleza Rice da ta kira shi ta wayar tarho game da kafa wannan doka ina ganin suna son yin anfani da shi ne,ganin y adage wannan batu to wane mataki zaa dauka agaba,wannan mataki shine yake baiwa Amurka tsoro mudai garemu kanfe na zabe zaa fara,amma KTT tana ganin dan mulkin kama karya ne cikin kakin soja yake mulkar mu ko zai ci gaba da mulki,to ababen dake faruwa ken an.
Jamian gwamnatin kasar dai sunce Mushharraf bai sanya hannun kan dokar bace saboda baya son hana ruwa gudu a harkokin zabe na kasar