1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Hamas ta sako mata biyu tsoffi

October 24, 2023

Hamas ta sako biyu daga cikin mutane 220 da ta ke yin garkuwa da su dab da lokacin da fada ke kara yin muni tsakanin Isra'ila da mayakan kungiyar.

https://p.dw.com/p/4Xw8R
 Yocheved Lifshitz
Yocheved LifshitzHoto: Jenny Yerushalmy/Ichilov hospital/AP/picture alliance

Kungiyar Hamas wacce kasashen yammacin duniya suka ayyana a matsayin kungiyar 'yan ta'adda ta sako biyu daga cikin mutanen da ta yi garkuwa da su a yayin harin da ta kai wa Isra'ila a ranar bakoye ga watan Oktoba a daidai lokacin da Amurka ta bukace ta da ta gaggauta sakin illahirin mutanen da ke hannunta domin hawa kan tebirin tattaunawa.

Karin bayani: Mayakan Hamas sun gaggari Isra'ila

Tun da farko dai shugaba Joe Biden na Amurka ne ya ce dole sai Hamas ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su sannan za a fara maganar neman mafita kan warware wannan sabon rikici ke ci gaba da lakume rayuwankan mutane.

Karin bayani: Harin bam ya haddasa mace-mace a asibitin Gaza

Sakin mutanen biyu dukanninsu mata kuma 'yan kasar Isra'ila da suka hadar da guda mai shekaru 85 da guda kuma mai shekaru 79 na zuwa ne kwanaki uku bayan sakin wata ba'Amurka da 'yartaa karshen makon jiya. 

Akalla dai mutane 220 ne ake kyautata zaton kungiyar ta Hamas ke yin garkuwa da su a yayin harin na bazata da tai kai wa Isra'ila.

Karin bayani: Isra'ila za ta shiga sabon babi na yaki a Zirin Gaza

A daya gefe kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macro ya isa birnin Tel Aviv a domin jaddada goyon baya ga Isra'ila a rikicin da take da kungiyar ta Hamas a zirin Gaza wanda kawo yanzu ya yi ajalin fararen hula 5.087 ciki har da yara  2.055 a zirin Gaza kamar yadda sabbin alkaluman Hamas ta fitar