Hana tofa albarkacin baki a Yuganda
May 6, 2016Ranar Alhamis mai zuwa 12 ga watan Mayu za a sake rantsar da Shugaba Yoweri Museveni wanda ya shafe shekaru 30 kan madafun iko, amma tuni 'yan adawa suka sanar da jerin matakan da za su dauka da suka hada da zanga-zanga saboda nuna rashin amincewa da magudin da aka tafka yayin zaben watan Fabrairu. Ministan yada labarai Manjo Janar Jim Muhwezi ya tabbatar da haramta nuna zanga-zangar 'yan adawar kai tsaye:
"Mun tsayar saboda umurnin kotu wanda ya hana nunawa kai tsaye."
Babbar jam'iyyar adawa ta Forum for Democratic Change ta nuna tirjiya kan sake rantsar da Museveni kan madafun iko a wannan wata.
Yanzu gwamnatin Shugaba Museveni ta haramta zanga-zanga da hana kafofin yada labarai nunawa, a cewar ministan yada labarai Muhwezi:
"Idan akwai umurnin da ya hana Dr. Kizza Besigye wanda ya nuna tirjiya, idan aka ba shi damar magana kai tsaye ga duniya baki daya an saba umurnin ke nan."
Babban dan takara na adawa a zaben shugaban kasa Dr. Kizza Besigye na karkashin daurin talala saboda watsi da sakamakon zaben da ya bai wa Shugaba Yoweri Museveni nasara a watan Fabrairu.
Masana shari'a a kasar kamar Nicholas Opio na watsi da matakin gwamnatin kan kafofin yada labarai.
Ita dai jam'iyyar adawa ta Besigye ta sha alwashi hana sake rantsar da Shugaba Yoweri Museveni kan madafun ikon kasar ta Yuganda.