Hannun ma'aikatar harkokin waje a ta'asar Nazi
October 26, 2010Shugaban tawagar binciken Eckart Conze ya musulta ma'aikatar ta harkokin waje tamkar wata ƙungiya ta miyagun laifuka, wadda ta rufa wa ɗanyyen mulkin 'yan Nazi baya. Ma'aikatar dake da mazauninta a Wilhelmstraße a birnin Berlin, bisa saɓanin yadda take iƙirari, ba wani abin da ta taɓuka na adawa da manufofin 'yan Nazi a wancan lokaci. A maimakon haka ma dai da yawa daga jami'an diplomasiyyarta sun yi madalla da ƙwatar mulki da Hitler yayi a shekara ta 1933, in ji Eckart Conze. Kuma daga bisani ma'aikatar ta wayi gari a matsayin wata cibiyar dake da hannu a ta'asar 'yan Nazi. An samu jami'an diplomasiyya dake da hannu a ta'asar da kuma wasu 'yan rakiya a tsakaninsu. 'Yan ƙalilan ne daga cikinsu suka janye kansu ko kuma suka bayyana adawa da lamarin, kamar yadda shugaban tawagar binciken ya nunar.
"Ma'aikatar harkokin waje ta tsoma hannunta a ɗanyyen mulkin 'yan Nazi tun daga 1933. Ta shiga dumu-dumu aka dama da ita wajen farauta da kisan gilla akan Yahudawa a duk faɗin Turai. A taƙaice ma'aikatar ta kasance wata ƙungiya ta 'yan miyagun laifuka."
Sakamakon binciken dai yayi nuni da cewar babban jami'in diplomasiyya, wanda kuma daga bisani aka naɗa sakataren ƙasa, Ernst von Weizsäcker, mahaifin tsofon shugaban ƙasar Jamus Richerd von Weizsäcker na da hannu a wannan ta'asa. A matsayinsa na Manzon Jamus a Switzerland ya sa ido wajen ganin lalle an tuɓe marubucin adabin nan na Jamus Thomas Mann daga ɗan ƙasancinsa sakamakon kakkausan sukan da yake wa 'yan Nazi. Shi dai Ernst von Weizsäcker na daga cikin wasu jami'an diplomasiyyar Jamus 'yan ƙalilan da aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai gidan kurkuku bayan yaƙin duniya na biyu sakamakon hannu da suke da shi a manufofin siyasar 'yan Nazi. Sai dai kuma ma'aikatar ta harkokin waje tayi bakin ƙoƙarinta wajen toshe gaskiyar lamarin da ma taimakawa wajen yi wa masu miyagun laifuka na yaƙi da ake nema ruwa a jallo, gangami da hana damar farautarsu. Kimanin shekaru huɗu tawagar masana tarihin suka yi suna gudanar da bincikensu. Bisa ga ra'ayin Moshe Zimmermann daga Isra'ila dake ɗaya daga cikin tawagar rawar da ma'aikatar harkokin wajen ta taka ta zama kyakkyawar misali game da yanayin da illahirin al'umar Jamus suka kasance a cikin ƙarƙashin mulkin 'yan Nazi:
"Al'umar Jamus ta kasance tamkar wata gamayya ce ta 'yan miyagun laifuka tsakanin 1933 zuwa 1945 kuma ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ta'asar ita ce ma'aikatar harkokin waje. Kazalika ma da ma'aikatar kuɗi da ta sufurin jiragen sama. Matsalar, kamar yadda sakamakon binciken ya nunar, ita ce ta rashin nagartar tubalin da aka gina mulkin akansa, wanda ya shafi ƙabilanci da wariyar jinsi."
Ministan harkokin waje Guido Westerwelle yayi maraba da rahoton tawagar binciken, wanda ya ce kundi ne na tarihi mai muhimmancin gaske, wanda nan gaba zai iya zama wani ɓangare na koyar da ayyukan diplomasiyya.
"Abu ne dake da ban tsaro ganin gaggan jami'an diplomasiyya na da hannu a ɗanyyen mulki da kama karyar 'yan Nazi. A ɗaya hannun kuma akwai sunayen wasu mutanen da ba a sansu ba, waɗanda suka nuna jarunta wajen ba wa Yahudawa kariya. Wannan dai wata mahawara ce da za a daɗe ana yinta."
Tsofon ministan harkokin waje Joschka Fischer shi ne ya kafa wannan tawaga a shekara ta 2005 sakamakon saɓanin da aka fuskanta game da juyayin jami'an diplomasiyyar da suka gabata.
Mawallafi: Bettina Marx / Ahmad Tijani Lawal
Edita: Umaru Aliyu