1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta hada kai da kasashe 11 na Afirka ta Yamma

Salissou Boukari
November 22, 2016

Faransa tare da hadin gwiwar wasu kasashe 11 na Afirka ta Yamma sun sha alwashin gama karfi wajen yakar 'yan ta'adda da ke zama wata babbar barazana ga yankin Sahel da kuma kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/2T4Zx
Frankreich Bernard Cazeneuve in Paris
Hoto: Getty Images/AFP/M. Alexandre

A wani mataki na samun karin ilimi kan yaki da 'yan ta'addan, ministocin cikin gidan ko kuma na tsaro na kasashen 11 na yammacin Afirka, sun halarci wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu tare da ministan cikin gidan kasar Faransa Bernard Cazeneuve a birnin Paris na kasar Faransa.

Da ya ke magana kan wannan batu, ministan cikin gidan kasar ta Faransa Cazeneuve ya ce sun kara tabbatar wa juna da aniyarsu ta aiki tare domin yakar duk wani nau'i na ta'addanci, inda ya kara da cewa yakin da ake da 'yan kungiyar Al-Qaida a yankin Sahel ta AQMI na da babban maimmanci har ma ya tabo irin rawar da sojojin Faransa ke takawa a kasar Mali tun daga shekara ta 2013.

Kasashen na yammacin Afirka dai sun fuskanci tarin matsaloli, inda birnin Bamako ya fuskanci hari na ran 20 ga wata Nuwamba 2015, Burkina Faso a ran 15 ga watan Janairu farkon wannan shekara yayin da Cote d'Ivoir da harin Gran Bassam na ran 13 ga watan Maris 206 da kuma Nijar inda aka kai harin Bosso a ranar uku ga watan Yuni na wannan shekara da ya halla sojoji fiye da talatin.