Haramcin sanya nikabi a makarantun Masar
September 12, 2023A cikin sabuwar doka da jaridar gwamnatin Masar ta Akhbar al-Youm ta buga, fadar mulki ta Cairo ta kayyade kayan makaranta da daliban firamare da sakandare ya kamata su sanya tare da haramta rufe fuska. Sai dai 'yan Masar sun nunar da cewar hauhawar farashin litattafan da karancin guraben karatu da kayan aikin malamai ne ya kamata gwamnati ta maida hankali a kai maimakon haramta nikabi.
Karin bayaniMartani kan hana sanya Hijabi ko Nikabi:
Duk da cewa galibin matan Masar na amfani da mayafi wajen lullube jikinsu, amma dai tsiraru ne ke amfani da nikabi a wannan kasa mai yawan Musulmi. Wasu daga cikin 'yan Masar sun fusata saboda gwamnati ba ta bayar da hujjar haramta nikabi ba, amma wasu sun danganta shi da matakin yaki da tasurin ra'ayin Islama.