Mahukunta a Burundi sun sanya dokar haramta zanga-zanga
May 11, 2015Talla
Macin dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da mahukuntan Burundi suka bayar da umurnin haramta duk wata zanga-zanga a kasar. Al'ummar Burundi dai sun kwashe tsahon kwanaki suna zanga-zanga a kan tituna domin nuna adawarsu da shirin yin tazarce a karo na uku da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya kudiri aniyar yi, kudirin da suka ce ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.
A karkashin kundin tsarin mulkin Burundi dai wa'adin mulki biyu na shekaru biyar ne shugaban kasa ke da damar yi. Nkurunziza ya dage kan cewa yana da damar tsayawa takara a karo na uku kasancewar 'yan majalisar dokokin kasar ne suka zabe shi a karon farko wanda ya ce hakan ya ba shi damar tsayawa karo na uku.