1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramtaccen zabe a Ukraine?

Halimatu AbbasSeptember 3, 2012

Julia Timoschenko, tsohuwar fraministar Ukraine da yanzu ke a gidan wakafi ta sake yin yi kira ga Kungiyar Tarayyar Turai da ta taimaka a dangane da zaben da zai gudana a kasar a watan Oktoba

https://p.dw.com/p/162x8
(FILE) A file photograph taken 11 March 2010 of former Ukrainian prime minister and opposition leader Yulia Tymoshenko speaks during a press conference in Kiev, Ukraine. Yulia Tymoshenko former Prime Minister of Ukraine was sentenced to seven years in prison after she was found guilty of abuse of office when brokering the 2009 gas deal with Russia. EPA/SERGEY DOLZHENKO (zu dpa: "Spannung in Straßburg: Gerichtshof verhandelt Fall Timoschenko" vom 27.08.2012) +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Hoto: picture-alliance/dpa

A cikin hira da mujallar Newsweek ta kasar Poland ta yi da ita ta ce yanzu ya kamata a samu wannan taimako amma ba bayan zaben ba. Timoscheko ta zargi shugaba Viktor Janukowitsch da kafa tsarin kama karya a kasar ta Ukraine. Kuma tuni ta bayyanar da sakamakon zaben na watan Okotoba a matsayin murdadde. T ace Janukowitsch shi ne ke ikon kotuna da 'yan sanda da ma'aikatu da kuma mafi yawa daga cikin kafafen yada labarun kasar. Ita dai tsohowar fraiministar da ke fama da ciwo mai tsanani tana zaman gidan yari na shekaru bakwai bisa laifin yi ba daidai ba. Kasashen yamma da dama sun soki wannan hukunci suna masu cewa hakan na da nasaba ne da dalilai na siyasa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan Ladi Aliyu