Hare-hare a gabashin Ghouta na Siriya a cikin hotuna
An kashe daruruwan mutane a cikin daya daga cikin hare-haren boma-bamai na gwamnatin Siriya mafi muni tun lokacin yakin ya fara a shekarar 2011. DW ta duba irin asarar da farmakin ya haddasa a cibiyar 'yan tawayen.
Mako daya na hare-hare
Sama da mutane 500 aka kashe a daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai a gabashin garin Ghouta kusa da Damascus tun lokacin da aka fara yakin a 2011. Dakarun Shugaba Bashar Al Assad sun ci gaba da kai hare-hare a gabashin Ghouta duk da matakin da MDD ta dauka na tsagaita wuta da kwanaki 30, haka kuma da yarjejeniya tsagaita wuta ta kwanaki biyar da shugaba Vladimir Putin ya amince da ita.
'Jahannama cikin kasa'
Da yake magana a game da hare-haren da Siriya ta kai a ranar 19 ga watan Febrairu babban sakataran MDD Antonio Guterres ya bukacin wannan barin wuta da a dakatar da shi. Gabashin Ghouta nan ne sansani na karshe na 'yan tawayen Siriya inda ke da mutane kimanin dubu 400, wanda yawancinsu suka gaza yin gudu. Damascus na son ta ci yaki, tare da taimakon Rasha, domin kare muradunta a tattaunawa.
Rahotannin a kan hare-hare da makami mai guba
A cewar masu gwagwarmaya da likitoci na yankin, jama’a da dama na fama da cututuka wadanda hare-hare da makami mai guba ke haddasawa wadanda aka kai wa harin an yi musu magani a asibiti. Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gargadi gwamnatin Siriya cewar yin amfani da makami mai guba na iya janyo martanin Fraransa, sai dai kuma gwamnatin Siriya ta musunta yin amfani da makamin.
Mutane dubu 300 aka kashe
Baba da yaro na kallon sauran da aka harbo a Douma, lardi mafi girma na gabashin Ghouta. Sama da mutane dubu 300 aka kashe tun lokacin da aka fara yakin a 2011, lokacin da gwamnatin ta fatataki masu zanga-zanga da suka bukaci a saki fursunonin siyasa kana shugaba Bashar Al Assad ya yi marabus.
'Rashin abinci mi gina jiki ya karu da gaggawa'
Masu fafutuka na cewar al’ummar Douma na fama da karancin abinci da ruwan sha. Marten Mylius shugaban ayyukan jin kai na kungiyar CARE a yankin Gabas ta Tsakiya ya shaida wa DW ''Bayan lalata hanyoyin wucewa frashin kayan abinci ya yi tashi. Kilo daya na shimkafa dala 4,50 misali (€3.66). Abin da ya kara janyo matsalar abinci mai gina jiki da gaggawa.''
'Jama'a' gwamnatin ta yi watsi da su'
Shiga gabashin Ghouta ya yi wahala babu hanya mai zuwa kai tsaye daga Idlib, sai dai ku shiga daga Turkiya, Masu kai agaji ba su iya shiga sai dai su tsaya bakin boda saboda akwai wahala dole sai sun daidaita da gwamnatin Siriya a cewar Mylius.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a tsagaita wuta
A ranar 24 ga watan Faibreru kwamitin sulhu na MDD gabaya ya bukaci da a tsagaita wuta na kwanaki 30 a Siriya. Kuwait da Sweden, sun ba da shawara da a tsagaita wuta da kwanaki 30 a yakin da ake yi daukacin kasar domin isar da kayan abinci da magunguna. Sai dai Rasha ta bukaci ka da a tsaida wutar da Al-Qaida da kuma kungiyar IS .