Hare-hare a Pakistan
July 15, 2007Kwanaki 3, bayan murƙushe yan takife, a harabar jan majallacin Islamad, wasu yan ƙunar baƙin wake sun kai hare-hare a arewa maso yammacin Pakistan.
Wannan hari, ya yi sanadiyar mutuwar mutane, a ƙalla 30, mafi yawan su jami´an tsaro
Miniitsan cikin gidan Pakistan, Aftab Ahmed Sherpao, ya danganta wannan al´ammari da rikicin Lal Massajid, wanda ya hallaka mutnae 75 a cikin wannan mako, a birnin Islamad
Ba´ada bayan wannnan hare-hare, ƙungiyoyin kishin addinin Islama, a yankin Waziristan, sun bayana roshewar yarejeniyar sulhu, da su ka cimma tare da gwamnatin Pakistan.
Majalisar Choura, ta wanan yanki ,ya yanke shawara russa yarjejeniyar, a sakamakon dura mikiyar da sojojin gwamnati su ka yi wa jan massalaci.
Sannan majalisar ta ɗauri aniyar shirya sabin hare-hare, tare da tura ɗauki ga yan taliban na ƙasar Afghanistan.