1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Hare-hare sun dakatar da karatu a Nijar

March 27, 2021

Sama da kananan yara dubu 22 ba su zuwa makaranta a Nijar, yayin da wasu mutanen kuma sama da dubu 100 ke zaman hijira saboda hare-haren 'yan bindiga a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/3rGIf
Niger Agadez Afrika
Hoto: Imago/alimdi

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce sama da kananan yara dubu 22 ke zaune ba su zuwa makarana a Nijar, yayin da wasu mutanen kuma sama da dubu 100 ke zaman hijira sakamakon ayyukan 'yan bindiga.

Daga watan Janairun wannan shekara dai an rufe makarantu 312 a yankin, abin da ya shafi 'yan mata sama da dubu 10 daga cikin jimillar yaran da ke zaune ba tare da karatun ba.

Galibin wuraren da matsalar ta fi shafa dai suna yankin Tillaberi ne da ke iyakar Nijar din da kasashen Mali da Burkina Faso, yankunan da mayakan tarzoma masu alaka da kungiyar al-Qaeda da na IS ke sheke ayarsu.

Karamar kasar ta yankin yammacin Afirka, ta yi asarar rayukan daruruwan 'ya'yanta, yayin da jami'an wasu miliyoyon suka rasa sukuna, ga kuma uwa-uba irin tsananin da talakawan kasar ke fuskanta ta fuskar tattalin arziki.

Kusan hare-hare 300 ne aka samu a yankin na Tillaberi a bara kadai a Nijar din.