An yi tir da harin kunar bakin wake a Indonesiya
May 15, 2018Iyalan gida guda me mutane shida sun kai hari kan mabiya addinin Kirista marasa rinjaye a majami'u uku a Surabaya birni na biyu mafi girma a Indonesiya, inda suka janzo rasa rayukan mutane akalla 13 baya ga raunata wasu 40 kamar yadda jami'an kasar suka bayyana. Cikin wannan iyali dai masu kai hari har da yara 'yan mata daga shekaru tara zuwa 12. Har ila yau rahotanni sun nunar da cewa maharan sun fito ne daga cikin wadanda suka mara baya ga mayakan IS su 500 da suka dawo daga Siriya.
A wannan Litinin ma an kai wani harin da shi ma ake zargin wasu iyalan da kai shi, kamar yadda Tito Karnavian shugaban 'yan sanda a Indonesiya ya yi karin bayani.
"A bayyane take mun fitar da sunayen wadanda ake zargi da hannu a harin, wadanda aka bayyanasu da sunan "TM" su ma dai daga iyali guda suke, uwa da uba da yaransu daya daga ciki ta rayu."
Maharan a ababen hawa sun tashi bam a hedkwatar 'yan sanda ta birnin Surabaya na kasar ta Indonesiya a wannan Litinin, lamarin da ya jaza raunika ga mutane 10 ciki kuwa har da jami'an 'yan sanda hudu kamar yadda 'yan sandan suka bayyana. Harin da ke zuwa akufe-akufe ya sanya Shugaba Joko Widodo na Indonesiya ya nemi 'yan majalisar kasar su sake nazari kan dokar da ta shafi ta'addanci, yana mai cewa.
"Ina kira ga 'yan majalisa da sauran sashi na gwamnati da abin ya shafa su sake nazari kan dokar ta'addanci da muka gabatar a watan Fabrairun 2016, ya kamata a kammala aiki kan wannan doka cikin hanzari, hakan zai taimaka wa jami'an tsaro a aikinsu."
Tun kai harin na majami'ar da ke a birnin na Surabaya shugabanni da al'ummomi na kasa da kasa ke aika wa shugaba Widodo jaje ciki kuwa har da masu makobtaka da kasar. Julie Bishop ita ce ministar harkokin wajen Ostireliya.
"Mutane da ba su ji ba su gani ba an halaka su a wannan hari, gwamnmatin Ostireliya na aiki tare da gwamnatin Indonesiya na ganin wadanda ke kitsa irin wannan hari an hukuntasu, hakazalika za mu ci gaba da aikin hadin gwiwa wajen ganin an karya lago na alakar 'yan ta'addar. Muna alhini ga wadanda suka mutu, wadanda suka samu raunika muna fatan su samu lafiya, kuma za mu ci gaba da kokari wajen ganin ba a samu irin wannan ba a kasar Ostireliya."
Su ma dai al'ummar wannan birni na Surabaya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da hare-haren kamar yadda Achmad Machmudi ke cewa.
"A matsayina na dan wannan kasa kuma Musulmi na yi Allah wadarai da wannan hari da babu ko shakka 'yan ta'adda suka kai shi, addu'ata ita ce ina fatan jami'an tsaro da duk wadanda alhakin tsaro ya rataya a wuyansu za su yi abin da ya dace kan wannan."
Tuni dai kungiyar nan ta Jamaah Ansharut Daulah (JAD) da ke mubaya'a da kungiyar IS ta dau alhaki na hare-haren, yayin da daga bangaren mahukunta ministan tsaro ya ce 'yan sanda za su samu mara baya na sojoji don tabbatar da tsaro a wannan kasa da tafi yawan al'ummar Musulmi a duniya.