1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren mayar da martani na ci gaba a Damaskus

Mohammad Nasiru Awal
March 21, 2017

Ana ci-gaba da fafatawa tsakanin dakarun gwamnatin Siriya da na 'yan tawaye da ke kokarin kutsawa birnin Damaskus.

https://p.dw.com/p/2Zdb9
Syrien Krieg - Kämpfe in Damaskus
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/A. Suleyman

Dakarun gwamnatin Siriya sun kaddamar da sabon hari kan mayakan 'yan tawaye a birnin Damaskus, biyo bayan wasu tagwayen hare-hare daga bangaren 'yan tawaye da sanyin safiyar wannan Talata. Wannan dai shi ne yunkuri na biyu da 'yan tawaye suka yi cikin kwanaki uku a kokarin kutsawa cikin birnin na Damaskus. Faya-fayen bidiyo daga kafar yada labaru karkashin ikon rundunar gwamnatin Siriya sun nuna yadda hayaki ya tirnike sararin samaniyar unguwar Jobar da ke hannun 'yan tawaye. Da farko kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta ce 'yan tawayen Siriya sun tada bam cikin wata mota a wata unguwa da ke gabacin Damaskus kafin su kaddamar da wani sabon hari kan babban birnin na Siriya daga unguwar Jobar. Hezbollah dai na mara wa shugaban Siriya Bashar Assad baya a yakin basasar kasarsa.