1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Rasha ta yi ruwan bama-bamai a Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou
December 30, 2023

Hukumomi a Ukraine sun yi ga kasashe kawayen kasar da su kara azama wajen kai musu daukin da zai kai su ga dakile muggan hare-haren Rasha a kokarinta na mamaye kasar.

https://p.dw.com/p/4aimL
Ukraine I Jami'in kwana-kwana na kokarin kashe gobara bayan harin Rasha I Yankin Charkiw
Ukraine I Jami'in kwana-kwana na kokarin kashe gobara bayan harin Rasha I Yankin CharkiwHoto: Yevhen Titov/REUTERS

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Telegaram, wani babban jami'in gwamnatin kasar Andriï Lermak, ya ce duniya na ganin halin da kasar ta fada, kana hare-haren baya-bayan nan da Rasha ta kai, na nuna irin tsananin bukatar da ke da akwai na kawo musu dauki.

Karin Bayani: Jamus ta ce diflomasiyya ce mafita a yakin Ukraine

Kimanin mutane 30 ne dai aka tabbatar da sun mutu, bayan wani luguden wutar dakarun Rasha a yankunan Ukraine ciki har da babban birnin Kiev, harin da ke zama irinsa mafi muni a cewar gwamnatin Ukraine, an kuma ruwaito mutane akalla 160 da suka jikkata a hare-haren da ma'aikatar tsaron Rashar ta tabbatar.

Karin Bayani: Shugaba Putin ya sanar da nasara a yakin Ukraine

Tuni ma dai shugaban kasar Volodymyr Zelensky, ya ziyarci dakarunsa a fagen dagar mai cike da hadari, a nata bangare ita kuwa kasar Poland da ke zaman memba a kungiyar tsaro ta NATO, ta zargi Rashar da yi wa sararin samaniyarta kuste da makamai masu linzami, tare da kira ga Rashar da ta dakatar da yakin da ta ke yi a Ukraine.