Hare-haren ta'addanci a Turai
Hare-haren ta'addanci da aka kai a birnin Brussels na kasar Beljiyam ya kara sanya Turai cikin firgici. Sama da shekaru 10 ke nan hare-haren bama-bamai ya girgiza Turai. Wani abu da ya za ma daki-daki.
Istanbul: Nuwamba 2003
Cikin kwanaki biyar 'yan ta'adda masu kishin addini sun kai hare-haren bama-bamai a Istanbul. Mutane 58 ne suka mutu yayin da wasu sama da 600 suka jikkata. A ranar 15 ga watan 11 tagwayen bama-bamai suka fashe a wajen ibadar Yahudawa. A ranar 20 ga watan na 11, wasu mahara biyu suka kai hari a kan wani banki na Birtaniya da kuma ofishin jakadancinta. An yanke wa maharan hukunci a shekara ta 2007.
Madrid: Maris 2004
Yayin da aka kai harin ta'addanci mafi muni a tarihin Spain, mutane 191 ne suka mutu kana sama da 1800 suka jikkata. Bama-bamai masu yawa ne suka fashe a ranar 11 ga watan Maris a jiragen kasa daban-daban guda hudu, har ma da tashar jiragen kasa ta karkashin kasa. An yanke wa maharan hukuncin daurin shekaru 43.000 a gidan kaso. Wani hukunci abin kwatance. Za su yi sama da shekaru 40 a gidan kaso.
London: Yuli 2005
A ranar bakwai ga watan Yulin shekara ta 2005 a lokacin da aka fi zirga-zirgar ababen hawa, masu kaifin kishin addinin Islama hudu suka kai harin kunar bakin wake a babban birnin Ingila. A kusan lokaci guda uku suka tayar da bama-bamai a cikin jiragen kasa inda guda ya tayar a motar Bus. Mutane 52 ne suka mutu. Harin na zaman mafi muni da masu kaifin kishin addini suka kai a tarihin Birtaniya.
Denmark: Satumba 2005
A ranar 30 ga watan tara na 2005 Jaridar Denmark ta "Jyllands-Posten" ta buga hotunan barkwanci na addinin Islama guda 12. Guda daga ciki ya nuna hoton Annabi Muhammad da bam a kansa a matsayin rawani. Wannan ya janyo zanga-zanga a duniya baki daya. An kuma yi yunkurin kai hari a gidan jaridar. Bayan hari a kan gidan jaridar "Charlie Hebdo", kamfanin "Jyllands-Posten" ya tsaurara matakan tsaro.
Stockholm: Disamba 2010
Kwanaki kalilan da bukukuwan Kirsimeti, ranar 11 ga watan Disamba 2010 aka kai harin bam biyu a wata tasha mai zirga-zirgar motoci a babban birnin kasar Sweden. Mutane biyu ne suka jikkata sannan maharin mai kimanin shekaru 28 dan asalin kasar Iraki ya kashe kansa. Tsawon lokaci ana neman dan uwansa da ake zargin sun shirya kai harin tare, ana tsammanin ba shi kadai ba ne.
Paris: Nuwamba 2011
A shekara ta 2011 kamfanin jaridar "Charlie Hebdo" ya fuskanci hari. Wani da ba a sani ba ya jefa abubuwa masu fashewa cikin ofishin tace labarai na kamfanin. Babu dai wanda ya ji ciwo. Har yanzu ba a gano wanda ya kai harin ba. Ana tunanin an kai harin ne sakamakon sukan da jaridar ke yi wa addinin Musulunci. A sabo da haka jaridar ta sha fuskantar barazana. Ta dade karkashin kulawar 'yan sanda.
Toulouse: Maris 2012
Tsakanin 11 da 22 ga watan Maris na shekara ta 2012 sun kasance cikin fargaba. Da farko wani mutum a kan babur ya harbe wasu sojoji biyu. Kwanaki takwas bayan nan a ranar 19 ga watan na Maris wani mutum ya harbe dalibai uku da malaminsu a wata makarantar Yahudawa. Tsawon kwanaki 'yan sanda na neman sa. Daga bisani sun yi wa gidansa kawanya a ranar 22 ga watan na Maris inda suka cafke shi.
Brussels: Mayu 2014
Wani dan bindiga dadi ya bude wuta a ranar 24 ga watan Maris a wani gidan yawon bude idanu na Yahudawa a birnin Brussels tare da kashe mutane hudu. Da fari maharin dan kasar Faransa ya tsere, sai dai an kamashi a Faransan inda aka damka shi ga mahukuntan kasar Beljiyam. An ce ya zauna a Siriya tare da masu kaifin kishin addini, an ma taba tsare shi a gidan kaso bisa laifin fashi da makamai.
Brussels: Satumba 2014
A watan Satumbar 2014 an dakile wani hari da aka shirya kai wa a ofishin hukumar Tarayyar Turai da ke birnin Brussels. Kwararru sun ce har yanzu Turai na fuskantar barazanar harin ta'addanci daga masu kaifin kishin addini. A yanzu su na farautar 'yan ta'adda. Turawa da dama na zuwa Iraki da Siriya domin taya 'yan IS yaki, kana su dawo Turai da nufin aiwatar da wani abu a kan hukumominsu.
Paris: Janairu 2015
Mutane 12 ne suka kai hari a gidan jaridar barkwanci ta "Charlie-Hebdo" a Paris. Har yanzu ana farautar maharan da suka kware a kaifin kishin addini. Gwamnatin kasar Faransa ta bayar da sanarwar gagarumar barazana daga 'yan ta'adda. Shugaba Hollande ya yi tir da harin wanda ya bayyana da gagarumin aikin rashin imani.
Hari a kan 'yancin fadar albarkacin baki
Harin da aka kai a kan jaridar Charlie Hebdo hari ne a kan 'yancin fadar albarkacin baki da na yada labarai, a cewar 'yan jarida da 'yan siyasa. A ranar 7 ga watan 1 shekara ta 2015, wasu mahara sun hallaka babban editan jaridar. Ya sha fuskantar barazana kan labaran da yake bugawa. Kafafaen yada labaran Turai sun bayyana shi da mara tsoro wajen fafututkar kare 'yancin yada labarai.
Paris cikin firgici
Mutane 128 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 300 suka jikkata sakamakon jerin hare-haren ta'addanci da aka kai a birnin Paris. Hare-haren da kungiyar IS ta kai. Mahara masu yawa sun kai hare-hare kusan lokaci guda a gidajen cin abinci da gidajen kallo da na sayar da barasa.
Janairu 2016: Turkiya ta shiga rudani
Mutane da dama ne suka hallaka a wani harin ta'addanci da aka kai a dandalin Sultanahmet da ke kusa da wajen tarihin Romawa, da ke birnin Istanbul, birnin da ke karbar bakuncin 'yan yawon bude idanu. Daga cikin wadanda suka rasa ransu akwai Jamusawa 10. Ana zargin kungiyar IS da kai wannan hari.