hare-haren ta´danci a Pakistan
July 17, 2007Yankin Waziristan da ke arewancin Pakistan, ya shiga yanayin tashe-tashen hankulla, tun bayan murƙushe yan takifen Jan Massalaci a birnin Islamabad.
A sahiyar yau, a kalla sojojin gwamnati 4 su ka rasa rayuka,a yayin da dama su ka ji raunuka, a sakamakon hare-haren ƙunar baƙin wake da su ka rutsa da wannan yanki.
A tsukin yan kwanaki 3 da su ka wuce, kusan mutane 80 su ka kwanta dama, a cikin wannan tashe-tashen hankulla.
A halin yanzu, mutane da dama na ci gaba da ƙaura daga yankin Waziristan, a sakamakon sanarwar da majalisar Shura ta fiddo, inda ta bayyana kawo ƙarshen yarjejniyar sulhu da ta cimma tare da gwamnati.
A ranar jiya, shugaba Pervez Musharaf ya aika tawagar ta mussamman, da zumar ciwo kan majalisar Shura, ta lashe amen ta , saidai wannan yunƙuri ya ci tura.